(ABNA24.com) Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta sanar da cewa matakin rage yawan man fetur da kasashen mambobin kungiyar OPEC da abokan huldarta suka cimma bai shafe ta ba.
Da yake karin haske kan matakin da kungiyar ta OPEC ta sanar da cimmawa a jiya Litini, ministan man fetur na kasar Iran, Bijan Namdar Zangeneh, ya ce matakin bai shafi kasashen Iran da Venezuela wadanda ke fama da takunkumi ba da kuam kasar Libiya.
A jiya ne kasashe masu arzikin man fetur mambobin kungiyar OPEC, suka cimma daidaito a tsakaninsu da kuma abokan huldarsu, ta rage yawan man fetur da suke samarwa.
Matakin zai ba da damar daidaita kasuwar mai ta duniya, sannan ana sa ran ya farfado da farashin man zuwa dala 15 kan kowacce ganga cikin gajeren lokaci.
Farashin man fetur dai ya yi faduwar da ba’a taba ganin irinta ba a tsawon shekaru sakamakon matsalar annobar coronavirus da kuma sabakin dake tsakanin kasashen Saudiyya da Rasha.
/129